Category Archives: Trending

Gwamnatin Najeriya zata gina layin Dogo daga Badin zuwa Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan kwantiragin Dala biliyan 6 da miliyan 68 da wani kamfanin kasar China don gina layin dogo daga garin Badin zuwa Kaduna, daga cikin aikin layin dogon da ya tashi daga Lagos zuwa Kano. Wannan jawabi na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktar yada labaran ma’aikatar Sufuri Yetunde Sonaike…

Read more

Za a gudanar da bincike kan sace Sandar majalisa a Najeriya

Majalisun dokokin a Najeriya za su kafa kwamitin da zai binciki dalilin da ya sanya wasu tsageru suka yi kutse cikin zauran majalisar dattijai suka kuma sa ce sandar majalisar a ranar Larabar da ta gabata. Shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki ne ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala wani dogon zaman sirri…

Read more

Jam’iyyar ‘yan gurguzu ta SPD a Jamus ta zabi Andrea Nahles

Jam’iyyar ‘yan gurguzu ta SPD a Kasar Jamus ta zabi mace a karon farko a tarihinta a matsayin shugaba. Andrea Nahles tasha gaban ‘yar takara Simonne Lange a babban taro na musammun da jam’iyyar ta kira a jiya Lahadi a Wiesbaden da ke a yammacin Jamus. Nahles tana da manyan kalubale a gabanta na dinke rarrabuwar kawunan…

Read more

Ana zargin ‘yan siyasa da hannu a kashe-kashen manoma da makiyaya a Najeriya

Fadar shugaban kasa a Najeriya ta zargi ‘yan siyasa da shirya kashe-kashen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiyar kasar nan.Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja.Sanarwar ta ce akwai wata…

Read more