Category Archives: Labarai

Shugaba Muhammad Buhari zai sasanta rikici tsakanin Yan Sanda da Majalisa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya alkawarta daukar matakan da suka dace domin kamo bakin zaren dangane da wani sabani da ya bullo tsakanin babban Sufeton ‘yan-sandan da kuma shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki. Shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan jiya lokacin da ya ke zantawa da manema labarai…

Read more

Kungiyar hadin kan Arewa ta baiwa yan kabilar Igbo wa’adin barin yankin Arewa

Gamayyar kungiyar hadin kan Arewa a Najeriya da ta taba baiwa ‘yan-kabilar Igbo wa’adin barin yankin Arewa a bara, ta nuna rashin amincewarta kan matsayar da gwamnonin Arewa da ma Jam’iyyar APC suka dauka dangane da sake fasalin kasa. Sanarwar hakan na kunshe ne cikin jawabin bayan taro da mai magana da yawun kungiyar ta…

Read more

Gwamnatin Najeriya zata gina layin Dogo daga Badin zuwa Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan kwantiragin Dala biliyan 6 da miliyan 68 da wani kamfanin kasar China don gina layin dogo daga garin Badin zuwa Kaduna, daga cikin aikin layin dogon da ya tashi daga Lagos zuwa Kano. Wannan jawabi na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktar yada labaran ma’aikatar Sufuri Yetunde Sonaike…

Read more

Za a gudanar da bincike kan sace Sandar majalisa a Najeriya

Majalisun dokokin a Najeriya za su kafa kwamitin da zai binciki dalilin da ya sanya wasu tsageru suka yi kutse cikin zauran majalisar dattijai suka kuma sa ce sandar majalisar a ranar Larabar da ta gabata. Shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki ne ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala wani dogon zaman sirri…

Read more